Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da COVID-19 ta yi sanadin mutuwarsu a Amurka ya zarce 170,000
2020-08-17 10:33:59        cri

Cibiyar nazarin tsarukan kimiyya da injiniya ta jami'ar Johns Hopkins ta Amurka, ta ce yawan mutanen da COVID-19 ta yi sanadin mutuwarsu a kasar ya zarce 170,000.

Ta ce yayin da yawan mutanen da suka kamu da cutar ya zarce miliyan 5.4 a kasar, adadin wadanda ta yi sanadin mutuwarsu ya tashi zuwa 170,019 ya zuwa karfe 10 da minti 27 na daren jiya Lahadi, agogon GMT.

A cewar wani rahoto da kungiyoyi 2 masu kula da lafiyar al'umma a Amurka suka fitar, asibitocin kasar sun kara samun karuwar wadanda suka kamu da cutar, saboda yaduwarta a cikin al'umma.

Baya ga haka, wani sabon rahoton cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Amurka, ya ce daga watan Maris zuwa Yuli, adadin yara dake kamuwa da cutar ya yi ta karuwa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China