Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane kimanin dubu 200 sun mutu a sakamakon cutar COVID-19 a kasar Amurka
2020-09-11 14:49:39        cri

Mujallar Times ta kasar Amurka, ta wallafa babban labari a shafin ta na farko a jiya Alhamis, inda ta jera yawan mutanen da suka mutu a sakamakon cutar COVID-19 a kasar Amurka a kowace rana, tun daga ranar 29 ga watan Febrairu zuwa 8 ga watan Satumba, don tunasar da mutanen kasar yadda aka samu mutane dubu 200 da suka rasa rayuka a kasar sakamakon cutar. Kana a karshe, mujallar ta kara da rubutawa wani taken "Rashin nasarar Amurka".

Mai tsara wannan babban bangon John Mavroudis, ya yi fatan mutanen da suka manta da wannan cuta, za su farka, su kuma fahimta cewa kimiyya da fasaha, su ne dabarun daidaita wannan matsala.

Babban edita, kuma shugaban gudanarwa na mujallar Times, Mr. Edward Felsenthal, ya bayyana cewa, ya yi shawarwari tare da tsohon gwamnan jihar Pennsylvania Tom Ridge, wanda ya bayyana cewa, an ga yadda wannan cuta ta yadu a dukkan sassan duniya kamar wani wasan kwaiwayo mai tayar da hankali, don haka ya kamata a yi kokarin sauya yanayin dake ciki tun da wuri. Ya ce idan ba a yi sauyi ba, hakan zai zama abun kunya gare su da shugabanninsu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China