Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani Hanin Ga Allah Baiwa
2020-09-23 19:37:33        cri

Ya zuwa yanzu, cutar numfashi ta COVID-19 tana ci gaba da yin barna a sassan duniya. Baya ga hasarar rayuka, cutar ta kuma shafi kusan bangarori na rayuwa, kama daga tattalin arziki, harkokin wasanni, yawon bude ido, ayyukan hidima, da tsarin zamantakewar rayuwa, da makamantansu.

Sai dai kuma yayin da bullar annobar COVID-19 ta kara ta'azzara tsarin ilmin nahiyar Afirka, a daya hannu guda kuma nahiyar ta amfana matuka da hanyoyin fasahar sadarwa, wajen raya ilimi a lokacin da ake tsaka da yaki da cutar COVID-19. Wai a rashin Uwa ake yin uwar Daki.

Bincike na nuna cewa, da yawa daga kasashen nahiyar, sun lura da muhimmancin koyon ilimi ta amfani da na'urorin zamani, a lokacin da aka rufe kusan dukkanin makarantu, don dakile yaduwar cutar COVID-19 wadda ta tilastawa gwamnatoci daukar matakai na fifita gudanar da darussa ta na'urori, a kanana da manyan makarantu.

Manyan masu ruwa da tsaki a fannin ba da ilimi, da malamai daga kasashen Afirka 52 ne suka gudanar da aikin binciken. Sun kuma amince cewa, samar da manyan damammaki na amfani da fasahar sadarwa, ya saukakawa dalibai wajen daukar darussa, a gabar da aka dage shiga ajujuwa don daukar darussa. Kaza lika rahoton ya zayyana wadatacciyar wutar lantarki, da na'urorin koyo, da jari a fannin, tare da layukan intanet masu sauri, a matsayin ginshikan wanzar da koyo da koyarwa a Afirka, lokacin da aka rufe makarantu sakamakon bullar COVID-19.

Wannan ne ma ya sa hukumar gudanarwar ta AU ta jaddada cewa, akwai bukatar a bunkasa kirkire kirkire a dukkan fannonin ilmi, a kuma rungumi tsarin juyin juya halin fasahohin ci gaban zamani, domin kara tasirin bangaren da kuma tabbatar da ganin ba a bar wani rukunin marasa galihu a baya ba。

A kokarin ganin kwalli ya biya kudin sabulu, ya sa kungiyar AU ta kaddamar da wani shiri da zai duba hanyoyin samar da kirkire-kirkiren tsarin koyar da ilmi a duk fadin nahiyar Afrika, ta yadda za a samu damar rage illolin annobar ta COVID-19 a fannin ilmi. Kasancewar ilimi ginshikin zaman duniya.

Daga cikin sabon tsarin da ta kaddamar, hukumar ta AU ta bukaci a tallafawa shirin da kudi dalar Amurka dubu 100.

Sai dai a yayin da ake kokarin ceto harkar Ilimin nahiyar daga kubuta daga tasirin wannan annobar, masana na cewa kasashen Afirka da suka aiwatar da dabarun bunkasuwa ne kadai za su yi saurin tsira, daga tasirin COVID-19. Abin da malam Bahaushe ke cewa, iya kudinka iya shagalinka. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China