Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta raya sha'anin sararin samaniya ne domin samun zaman lafiya
2020-07-24 20:17:34        cri

Wang Wenbin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Jumma'a a nan Beijing cewa, sha'anin sararin samaniya da kasar Sin ke himmantu a kai, wani muhimmin bangare ne na kokarin da dan Adam ke yi wajen yin bincike da yin amfani da sararin samaniya cikin ruwan sanyi. Sin tana raya wannan sha'anin ne domin samun zaman lafiya.

A jiya ne, kasar Sin ta yi nasarar harba na'urar binciken duniyar Mars ta farko mai suna Tianwen-1 zuwa sararin samaniya. Wasu kafofin yada labaru na ketare suna ganin cewa, kasar Sin ta harbar na'urar ce domin neman kankane harkokin sararin samaniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China