Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu Amfani Da Waya Za su Biya Karin Kudi Sakamakon Kudurin Gwamnatinsu Na Haramta Kamfanin Huawei
2020-07-19 16:49:38        cri
Masu amfani da wayar salula a kasar Birtaniya ba su ji dadin wani kuduri da gwamnatinsu ta sanar a ranar 14 ga wata ba cewa, daga ranar 31 ga watan Disamban wannan shekara, za a haramta sayen sabbin na'urorin fasahar 5G da kamfanin Huawei na kasar Sin ke samarwa, kana nan da karshen shekarar 2027, za a cire dukkan na'urorin kamfanin daga tsarin fasahar 5G na kasar.

Gwamnatin Birtaniya ta dauki wannan mataki ne bisa hujjar tsaron kasa, matakin tamkar yin shisshigige a harkokin kasuwanci. Hakika cikin shekaru 20 da suka gabata, kamfanin Huawei ya shiga ayyukan kafa tsarin sadarwa na Birtaniya, inda ya samu amincewa da goyon baya daga abokansa na kasuwanci na Birtaniya, kamar kamfanin Vodafone LSE. Dangane da kudurin gwamnatin Birtaniya, kamfanin Huawei ya ce, matakin gwamnatin Burtaniya na haramtawa kamfanin ci gaba da aikin samar da fasahar 5G a kasar, abin takaici ne, kuma hakan ka iya yin barazana ga kokarin Birtaniyar na cin gajiyar wannan fasaha, da karin kudin amfani da fasahar da ma kara raba kai a fannin fasahar zamani.

Sanin kowa ne cewa, gwamnatin Birtaniya ta tsai da wannan kuduri ne sakamakon matsin lambar da kasar Amurka ta yi mata. Abin da ke nuna cewa, ba ta iya tsai da kuduri kan harkokin diplomasiyya da kanta. Ko da yake ya zuwa yanzu Amurka ba ta nuna wata shaida ba, amma tana shafa wa kasar Sin da kamfanin Huawei kashin kaji, ta cin zalin kamfanonin da suka fi ta ci gaban fasaha. Har ma ta yi wa wasu kasashe barazana don su hada kai da ita wajen haramta kamfanin Huawei yin kasuwanci.

A don haka wadannan kasashen Turai da Amurka ba su da karfin hali kan ci gaban fasaharsu. A baya dukkan na'urorin fasahar 2G ko 3G da aka yi amfani da su a kasar Sin, na'urori ne da Sin ta saya daga kasashen waje. amma ba ta dogaro da fasahar kasashen waje kawai ba. Ta yi kokarin raya fasaha da kanta. A kwanan ta samu ci gaban fasaha ta fannin aikin sadarwa. Duk da cewa kasar Sin tana tsayawa da kanta wajen bunkasa fasaharta, amma ba ta rufe kofar ga kasashen waje ba.

Kudurin da Birtniya ta tsai da, ya mayar da ita baya a fannin raya fasahar 5G, zai kuma kawo illa ga yadda take amfani da fasahar da kuma tsarin fasahar. A saboda haka, wajibi ne ta sake tunani sosai kan wasu batutuwan da ke shafar muhimman muradunta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China