Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Huawei: Matakin gwamnatin Burtaniya na soke aikin kamfanin na samar da fasahar 5G abin takaici ne
2020-07-15 10:35:00        cri

Kamfanin sadarwa na kasar Sin wato Huawei, ya bayyana a jiya Talata cewa, matakin gwamnatin Burtaniya na haramtawa kamfanin ci gaba da aikin samar da fasahar 5G a kasar, abin takaici ne, kuma hakan ka iya yin barazana ga kokarin Burtaniyar na cin gajiyar wannan fasaha, da karin kudin amfani da fasahar da ma kara raba kai a fannin fasahar zamani.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, mai magana da yawun kamfanin Huawei dake Burtaniya Ed Brewster, ya ce masu amfani da wayar salula a Burtaniya, ba za su ji dadin wannan labari ba. Yana mai cewa, maimakon a gano bakin zaren, amma sai gwamnatin ta dauki mataki maras dadi, a don haka ya bukace mahukuntan kasar, da su sake tunani. Ya ce, kamfanin Huawei na da tabbacin cewa, sabbin matakan haramcin da Amurka ta dauka kan kamfanin, ba za su shafi jurewa da tsaron kayayyakin da kamfanin ke samarwa a kasar ba.

A jiya ne dai, gwamnatin Burtaniya ta sanar da cewa, daga ranar 31 ga watan Disamban wannan shekara, za a haramta sayen sabbin na'urorin fasahar 5G da kamfanin Huawei ke samarwa, kana nan da karshen shekarar 2027, za a cire dukkan na'urorin kamfanin daga tsarin fasahar 5G na kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China