Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hidimar tauraron dan Adam na BeiDou ta tallafa wajen shawo kan kalubalen ambaliyar ruwa
2020-08-04 11:03:55        cri

Kakakin hukumar dake lura da hidimar taswira da tauraron dan Adam na BeiDou mallakar kasar Sin ke samarwa Ran Chengqi, ya ce hidimar tauraron dan Adam din ta taimaka matuka, wajen shawo kan kalubalen ambaliyar ruwa da aka fuskanta a sassan kasar Sin.

Mr. Ran wanda ya bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Litinin, ya ce hidimar tsarin aikin tauraron na BDS, ta tallafawa kasar wajen dakile matsalar kwararar hamada, da lura da musayar bayanai, da ba da gargadin gaggawa, da kuma sauyawa mutane matsugai.

Bisa matsayar sa a sararin samaniya, da kuma mahangarsa daga duniyar bil Adama, tsarin aikin tauraron BDS, na iya samar da hidimomi masu inganci kai tsaye, dake ba da damar shirya tunkarar ayyuka na gaba.

Kaza lika ta hanyar amfani da wasu kayayyaki masu nasaba da taurarin na BDS, ana iya yin hasashe kai tsaye, game da lalacewar yanayi ta yadda hakan zai taimaka wajen kwashe mutane da ka iya fadawa cikin yanayi na kaka-ni-kayi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China