Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan kasuwar kasa da kasa sun nuna kwarin gwiwa kan farfadowar tattalin arzikin kasar Sin
2020-08-30 17:24:14        cri

A shekarar da muke ciki, kasar Sin ta samu nasarar yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19, lamarin da ya nuna karfinta na raya tattalin arziki. Kwanan baya, kafofin yada labaru na kasar Amurka sun kaddamar da sakamakon bincike da ke cewa, 'yan kasuwar kasa da kasa sun nuna kwarin gwiwa kan makomar tattalin arzikin kasar Sin. Suna ganin cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai bunkasa ba tare da wata matsala ba.

Sakamakon bincike da kwamitin darektocin kula da harkokin kudi na duniya na CNBC ya gabatar a kwanan baya ya shaida cewa, darektocin sun fi nuna kwarin gwiwa kan makomar tattalin arzikin kasar Sin, gwargwadon makomar tattalin arzikin Amurka. Karo na farko ne manyan jami'an kamfanoni masu yawa suka fi nuna karfin zuciya kan tattalin arzikin kasar ta Sin cikin wannan bincike.

Kana kuma, Mike Henry, babban darektan CEO na kamfanin BHP Billiton, wanda shi ne kamfani mafi girma na hakar ma'adinai a duniya, ya bayyana yayin da yake zantawa da CNBC a kwanan baya cewa, yanzu haka tattalin arzikin kasar Sin yana farfadowa ba tare da wata matsala ba. Gwamnatin Sin ta dauki wasu matakai na kara azama kan tattalin arziki. Mun kiyasta cewa, wadannan matakai za su kara farfado da tattalin arzikin kasar a shekara mai zuwa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China