Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu gagarumin ci gaba a yaki da talauci ta hanyar sayen kayayyaki
2020-08-14 12:26:41        cri
Sayen kayayyaki da aka samar karkashin shirin yaki da fatara, wani muhimmin mataki ne wajen inganta shirin yaki da talauci. Kamar yadda sabbin alkaluman da ofishin kula da shirin yaki da talauci na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar suka nuna cewa, kawo yanzu, adadin cinikin da aka samu na sayar da kayayyakin da aka samar karkashin shirin yaki da fatara ya zarce kudin Sin yuan biliyan 100 a wannan shekara.

A cewar Wang Dayang, mataimakin daraktan sashen yaki da talauci tsakanin zaman al'umma na hukumar yaki da fatara na ofishin majalisar gudanarwar kasar, bangarorin da abin ya shafa suna tallata kayayyakin da ake samarwa karkashin shirin yaki da fatara ta hanyar karfafa gwiwar hukumomin gwamnati su sayen kayayyakin da aka samar da kuma samar da kasuwannin sayar da kayayyakin da aka samar karkashin shirin yaki da fatarar, wanda ya hada da zaburar da kamfanoni da kungiyoyin al'umma da su tallata kayayyakin da ake samarwa.

A cewar kididdigar baya bayan nan da sashen kula da shirin yaki da fatara na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar, ya zuwa yanzu, an samar da jimillar kayayyaki karkashin shirin yaki da fatara 76152 a larduna 22 dake tsakiya da yammacin kasar, inda suka yi cinikin sama da yuan biliyan 102.7. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China