![]() |
|
2020-08-20 10:06:43 cri |
Sai dai hukumar ta bayyana cikin rahoton da ta saba fitarwa a kullum cewa, a ranar ta Laraba an tabbatar da rahoton mutane 7 sun kamu da cutar wadanda suka shigo daga ketare.
Sanarwar ta kara da cewa babu rahoton sabon hasarar rai da aka samu wanda ke da nasaba da annobar a babban yankin kasar Sin.
Ya zuwa ranar Laraba, jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a babban yankin kasar Sin ya kai 84,895, wanda ya kunshi har da marasa lafiya 516 da ake ci gaba da kulawa da lafiyarsu, daga cikinsu akwai mutane 24 dake cikin yanayi mai tsanani.
Hukumar lafiyar Sin ta sanar da cewa, baki daya, an sallami mutane 79,745 bayan sun warke, sai kuma mutane 4,634 wadanda cutar ta kashe a babban yankin kasar Sin. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China