Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gao Fu: An yi min allurar rigakafin cutar COVID-19
2020-07-29 10:57:48        cri
Shugaban cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasar Sin Gao Fu ya bayyana a gun taron tattaunawa da kamfanin kiwon lafiya na Ali da kamfanin wallafa litattafai na Cell Press na kasar Amurka suka gudanar ta yanar gizo a ranar 26 ga wata cewa, an yi masa allurar rigakafin cutar COVID-19, yana mai cewa, hakan zai kara imanin jama'a kan allurar rigakafin.

Gao Fu ya kara da cewa, yayin da ake ci gaba da bincike kan allurar rigakafin cutar COVID-19, cibiyarsa tana yin nazari kan wadanda suka fi dacewa su fara amfana da allurar rigakafin, yara ko tsofaffi ko masu aikin ba da jinya.

A halin yanzu, an riga an gwada allurar rigakafin cutar COVID-19 guda 24 a kan jikin bil-Adama a matakai daban-daban a duniya, a cikinsu guda 8 sun fito ne daga kasar Sin, kuma suna kan gaba a duniya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China