Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Urumqi: Ana baiwa al'umma tallafin jinyar COVID-19 kyauta
2020-08-03 10:17:36        cri
Mahukuntan birnin Urumqi, fadar mulkin jihar Xinjiang dake arewa maso yammacin kasar Sin, sun sha alwashin ba da jinya kyauta ga wadanda ake hasashen sun harbu da cutar COVID-19, da ma wadanda suka harbu da ita amma ba su nuna alamu ba, a gabar da birnin ke fama da bazuwar cutar a baya bayan nan.

Da yake tabbatar da hakan, shugaban JKS na jihar mai lura da sashen tsaron lafiyar jama'a He Xinguo, ya ce matakin na da nufin tabbatar da cewa, wadannan rukuni biyu na mutane sun samu kulawar da ta kamata a kan lokaci, ba kuma tare da biyan wani kudi ba.

A ranar Asabar din karshen mako, birnin na Urumqi, ya bayyana harbuwar sabbin mutane 29 da aka tabbatar sun harbu da COVID-19, da kuma wasu karin mutane 9 da suka harbu ba tare da nuna alama ba.

Bisa jimilla, yawan masu dauke da cutar, da wadanda ke dauke da ita amma ba su nuna alama ba a Urumqi ya ragu cikin kwanaki 3 a jere, wanda hakan ke nuna cewa, matakan kandagarki da na shawo kan cutar da ake dauka a birnin na yin kyakkyawan tasiri, kamar dai yadda Sui Rong, daya daga manyan jami'an birnin ya tabbatar.

Ya zuwa Asabar, an samu jimillar mutane 569 da aka tabbatar suna dauke da cutar ta COVID-19 a Xinjiang, baya ga wasu 112 da ke dauke da ita ba tare da nuna alama ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China