Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin gwajin cutar COVID-19 a kasar Sin ya kai miliyan 4.84 a kullum
2020-08-05 15:49:52        cri

A ranar 5 ga wata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya yiwa manema labarai karin haske game da batun yawan gwajin kwayar cutar COVID-19 a kasar.

Ya zuwa karshen watan Yuli, gwajin cutar da ake gudanarwa a kowace rana a fadin kasar Sin ya kai miliyan 4.84, inda aka ware cibiyoyin gwaje gwajen cutar kimanin 4946, sama da jami'an lafiya 38,000 ne suke gudanar da aikin.

Kasar Sin ta raba kayayyakin aikin gwajin cutar kusan miliyan 200 da wasu kayan aikin sama da 12,000 wadanda aka tura asibitoci, da cibiyoyin dakile cutuka, da tashoshin aikin kwastam dake fadin kasar.

A halin yanzu, adadin kayayyakin gwaje gwaje da sauran kayan aikin da aka samar a kasar Sin yana da karfin biyan bukatun da ake da shi wajen tinkarar aikin kandagarkin annobar, kana kasar Sin ta amince a yi gwajin cutar ga dukkan mutanen da suka nuna sha'awar yi musu gwajin bisa radin kansu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China