Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An maida hankali ga jama'a da farko a yayin da ake kokarin yaki da cutar COVID-19
2020-07-29 15:57:28        cri
Bayan da cutar COVID-19 ka barke, bisa jagorancin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin dake karkashin shugaban kasar Xi Jinping, Sin ta ba da muhimmanci matuka ga rayuka da lafiyar jama'a.

A kokarin hana yaduwar cutar COVID-19, a ranar 23 ga watan Janairu, an dakatar da zirga-zirgar motocin bas-bas da jiragen karkashin kasa da jiragen ruwa da motocin dake dogon zango a birnin Wuhan, da rufe tashar jiragen sama da tashar jiragen kasa a birnin. Nazarin da manyan hukumomin nazari na duniya 15 suka yi, ya nuna cewa, matakan da aka dauka a birnin Wuhan sun rage yawan mutanen da za su kamu da cutar COVID-19 da fiye da dubu 700 a kasar Sin. Babban sakataren MDD António Guterres ya yi nuni da cewa, jama'ar kasar Sin sun ba da gudummawa ga dukkan al'ummar duniya ta hanyar sadaukar da rayuwarsu.

Bayan da aka kulle birnin Wuhan, an tura tawagogin ma'aikatan lafiya 346 da suka kunshi likitoci da nas-nas 42600 daga wurare daban daban na kasar Sin da sojojin kasar zuwa lardin Hubei don kare rayuka da lafiyar jama'ar da suka kamu da cutar COVID-19.

Yayin da ake tinkarar cutar COVID-19 a kasar Sin, kasashen duniya da dama su ma suna tinkarar yanayin, Sin ta ba da rahoto game da yanayin tinkarar cutar ga hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ba tare da bata lokaci ba, da abubuwan dake shafar kwayoyin cutar, da yin hadin gwiwa tsakanin masananta na magance cutar da na kasa da kasa. Hakan ya taimaka wajen magance yaduwar cutar a duniya, da kuma daukar alhakinta a matsayinta na babbar kasa.

A yayin taron kiwon lafiya na duniya karo na 73 da aka gudanar ta kafar bidiyo a ranar 18 ga watan Mayu, Sin ta gabatar da wasu manufofi bisa yanayin da ake ciki, da shirye-shiryen da ta tsara don tinkarar cutar, kana ta yi alkawari cewa, bayan da aka cimma nasarar nazarin allurar rigakafin cutar, duniya za ta amfana. Kana an kafa wurin ajiye kayayyakin jin kai na duniya a kasar Sin, da kafa tsarin hadin gwiwar dake tsakanin asibitocin Sin da Afirka, da daukar matakan sassauta biyan basusukan da aka baiwa kasashe masu fama da talauci, hakan ya shaida tunanin Sin na martaba ra'ayin jin kai na kasa da kasa.

Kasar Sin kasa ce dake daukar alhakinta a duniya, kuma za ta ci gaba da yin kokarin kare hakkin jama'arta a dukkan fannoni don sa kaimi ga raya sha'anin kiyaye hakkin dan Adam yadda ya kamata. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China