Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministocin kasashen Sudan da Masar sun yi shawarwari kan batun madatsar ruwan kasar Habasha
2020-08-16 16:54:38        cri
Jiya Asabar, Firaministan gwamnatin wucin gadin kasar Sudan Abdalla Hamdok da firaministan kasar Masar Mostafa Madbouly da ya kai ziyarar aiki a Sudan sun bayyana a birnin Khartoum, fadar mulkin Sudan cewa, akwai bukatar yin shawarwari domin kulla wata yarjejeniyar dake shafar batun farfado da madatsar ruwa ta kasar Habasha.

Mostafa Madbouly ya kai ziyarar aiki ta yini daya a kasar Sudan a jiya Asabar, kuma a yayin ziyarar tasa, shi da Abdalla Hamdok, da shugaban kwamitin 'yancin kan kasar Sudan Abdel Fattah Burhan sun yi shawarwari kan batutuwan dake shafar madatsar ruwa ta kasar Habasha da sauransu.

An gina madatsar ruwa ta kasar Habasha a kan kogin Blue Nile, dake kusa da yankin iyakar dake tsakanin kasar Habasha da kasar Sudan. A watan Yulin bana, kasar Habasha ta sanar da kammala aikin tara ruwa a madatsar ruwan a matakin farko. Lamarin da ya haddasa damuwar kasashen Masar da Sudan kan ko za su samu isasshen ruwa.

A shekarar 2015, kasashen uku sun taba sanya hannu kan wata sanarwa, domin nuna girmamawa ga juna game da yin amfanin ruwa cikin yanayin adalci, musamman ma a kogin Nile. Haka kuma, kasashen uku sun amince da ci gaba da yin shawarwari kan wannan batu, domin kulla cikakkiyar yarjejeniya game da batun madatsar ruwan. Kana, a ranar 3 ga watan Agusta na bana, kasashen uku sun fara sabon zagayen shawarwari kan madatsar ruwan ta kasar Habasha, bisa aikin shiga tsakani da kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU ta yi. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China