Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan da Masar da Habasha sun samu ci gaba a batun gina madatsar ruwa
2019-12-23 09:35:52        cri

Ministan albarkatun ruwa da noman rani na kasar Sudan Yasir Abbas, ya ce kasashen Sudan da Masar da Habasha, sun cimma manyan nasarori game da tattaunawa kan batun ginin babbar madatsar ruwan Habasha ko GERD a takaice.

Abbas ya bayyana hakan ne, bayan kammala taron ministocin kasashen 3 da ya gabata a birnin Khartoum. Ya ce taron wakilan sassan uku ya haifar da manyan nasarori, wadanda za su baiwa kasashen damar kara fahimtar juna. Ya ce kasashen 3 sun yi musayar takardun dake kunshe da matsayar su, game da yanayin tafiyar da ayyukan madatsar ruwan na shekara shekara.

A watan Maris na shekarar 2015 ne dai shugabannin Masar da Sudan da Habasha, suka sanya hannu kan kudurin daukar matakan cimma matsaya, game da aiki da madatsar ruwan ta GERD cikin hadin gwiwa.

A shekarar 2011 ne Habasha ta fara ginin wannan madatsar ruwa, ko da yake Masar dake dogaro da kogin Nilu wajen samun ruwa mai tsafta, ta rika nuna damuwa, cewa gina madatsar ruwan na iya shafar kaso mai yawa, na albarkatun ruwan da take samu duk shekara daga kogin Nilu.

An dai tsara kaddamar da wannan madatsar ruwa ta GERD, bayan kammala aikin ta cikin shekaru 3. Madatsar mai fadin sakwaya mita 1,800, za ta lakume kudi har dalar Amurka biliyan 4.7 (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China