2020-03-10 13:10:30 cri |
Da yammacin jiya Litinin, ministan harkokin sufuri na kasar Habasha Dagmawit Moges ya gabatar da rahoton bincike na wucin gadi game da hadarin jirgin saman kasar da ya yi hadari a ranar 10 ga watan Maris na shekarar 2019.
Bincike ya gano cewa, jirgin sama ya yi hadari ne sakamakon matsalar na'urar sarrafa jirgin saman samfurin 737Max, ba laifin kamfanin jirgin ko matukinsa ba ne, kamar yadda ake zargi tun farko.
A sa'i daya kuma, rahoton ya bayyana cewa, kamfanin Boeing bai horas da matukan jiragen saman yadda ya kamata ba, ta yadda za su lakanci na'urorin tsaron jirgin. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China