Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar tsaron Masar ta tattauna batun rikicin Libya da na gina dam din Habasha daga kogin Nilu
2020-07-20 11:39:26        cri
Majalisar tsaron kasar Masar NDC wanda shugaban kasar Abdel-Fattah al-Sisi ke jagoranta, a ranar Lahadi ta tattauna game da cigaba na baya bayan nan da aka samu kan batun rikicin kasar Libya da na gina madatsar ruwa don samar da hasken lantarki da kasar Habasha tayi daga kogin Nilu, fadar shugaban kasar ne ta tabbatar da hakan.

Majalisar tsaron ta NDC ta kunshi shugaban majalisar dokokin kasar, da firaminista, da ministan tsaron kasar, da babban hafsan sojojin kasar, da babban jami'in tattara bayanan sirri, da ministocin harkokin waje, da na harkokin cikin gida, da ministan kudin kasar, da kuma sauran manyan jami'an gwamnatin kasar.

A sanarwar da hakakin fadar shugaban kasar Masar Bassam Rady ya fitar yace, hukumar tsaron ta jaddada aniyar gwamnatin Masar wajen kawo karshen kaiwa duk wani dauki daga kasasshen ketare ba bisa ka'ida ba wanda galibi ke kara lalata yanayin tsaron da ake ciki a kasar Libya da kuma zama barazana ga makwabtan kasashe har ma ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.

A cewar Rady, NDC ta jaddada aniyar warware rikicin siyasar kasar Libya, kasancewar batun tsaron Libya wani muhimmin al'amari ne ga tsaron Masar da sauran kasashen larabawa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China