Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta karrama sojoji injiniyoyi na kasar Sin masu kiyaye zaman lafiya a Sudan
2020-08-01 17:09:38        cri
Majalisar Dinkin Duniya ta karrama sojoji injiniyoyi na kasar Sin guda 225 da suke gudanar da ayyukan shimfida zaman lafiya a yankin Darfur na kasar Sudan, da lambar yabo ta kiyaye zaman lafiya, har ma sun samu babban yabo daga tawagar UNAMID, wato shirin wanzar da zaman lafiya na hadin-gwiwar MDD da AU a Darfur.

A wajen bikin karramawar da aka yi, babban jami'in sojoji injiniyoyi na kasar Sin Li Meng, ya karanta umarnin bada lambar yabo da kwamandan tawagar UNAMID ya sanyawa hannu, inda kuma a cewar Li, karramawar ta kasance babban yabo na musamman da aka yi wa daukacin sojoji injiniyoyi na kasar Sin, da amincewar da aka nuna musu saboda ayyukan wanzar da zaman lafiya da suka gudanar cikin nasara.

Tun daga shekara ta 2007, kasar Sin ta soma tura sojojinta masu aikin injiniya zuwa yankin Darfur na kasar Sudan, domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya. A halin yanzu muhimman ayyukan da suke gudanarwa, sun hada da, shimfida hanyoyin mota, da kafa gidajen bada kariya, da kiyaye filin saukar jiragen sama da sauransu.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China