Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sinawa sun fi son sayayya ta intanet yayin hutun ranar ma'aikata na watan Mayu
2020-05-07 15:29:38        cri

Ranar 1 ga watan Mayu, rana ce ta ma'aikatan kasa da kasa, a kasar Sin tsawon ranakun hutun na bana ya kai kwanaki biyar wato daga ranar 1 zuwa 5, yayin da Sinawa suke wannan hutu, sun fi sha'awar yin sayayya ta intanet, alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, adadin kudin da kamfanonin kasuwanci suka samu ta hanyar sayar da kayayyaki ta intanet ya karu, musamman ma a fannin sayar da amfanin gona, kwararrun da abin ya shafa sun bayyana cewa, sannu a hankali kasuwar kasar Sin tana nuna karfinta, yanayin sayayya mai inganci na kasar Sin bai canja ba.

Sabbin alkaluman da babban kamfanin kasuwanci ta intanet na kasar Sin Jingdong ya gabatar sun nuna cewa, a cikin kwanaki biyar na farkon watan Mayu wato yayin da Sinawa suke murnar ranar ma'aikatan kasa da kasa, adadin kudin da kamfanin ya samu ta hanyar sayar da kayayyaki ta intanet ya karu da kaso 45 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2019, a cikin kayayyakin da aka sayar, adadin kayayyakin da aka samar a cikin kasar ta Sin ya karu da kaso 52 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, kana adadin amfanin gona da aka sayar ya karu da kaso 148 bisa dari, mai nazarin alkaluman kamfanin Jingdong Chen Yao ta yi mana bayani cewa,

"A cikin kwanaki biyar na farkon watan Mayun da muke ciki, duk da cewa, matasa wadanda shekarun haihuwa suka kai 20 zuwa 30 sun fi sha'awar yin sayayya ta intanet, amma adadin kudin da masu sayayya wadanda shekarun haihuwarsu suka kai sama da 36 ya karu a bayyane, kana adadin kudin da matsakaitan masu sayayya da tsofaffi suka kasha kan sayayya ta intanet ya karu matuka, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, a sa'i daya kuma, kalmomin "wurin samarwa da amfanin gona" da masu shiga intanet suka yi amfani da su yayin da suke neman kayayyaki suna da yawa, misali karamin lobster wato crayfish da ake samu a lardin Hebei da dankalin Turawa da ake samarwa a birnin Lipu na lardin Guangxi, da Chinese yam na gundumar Wen ta lardin Henan, da naman tunkiya na gundumar Yanchi ta jihar Ningxia mai cin gashin kanta ta kabilar Hui da sauransu sun fi samun karbuwa daga masu sayayya a bana."

Rahotannin sun nuna cewa, adadin kayayyakin da ake sayarwa ta dandalin kasuwanci da kamfanon Jingdong ya kafa domin samar da tallafi ga manoman dake yankunan fama da talauci ya karu da kaso 135 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, a ciki, adadin tsuntsaye da kwai da shayi da naman alade da na shanu da na tunkiya da kayan lambu da aka sayar ta dandalin yakaru har kaso 200 bisa dari.

Yanzu haka an yi nasarar dakile yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Sin, a don haka wasu Sinawa sun je yawon bude ido ta mota, alkaluman da kamfanin kasuwancin Suning ya fitar sun nuna cewa, tsakanin ranar 29 ga watan Aflilu da ranar 4 ga watan Mayu, adadin kayayyakin da ake amfani da su a mota da kamfanin ya sayar da su ta intanet ya karu da kaso 256 bisa dari idan aka kwatanta da watan da ya gabata, kana tantuna, da tabarman leda da ake cin abinci a kan filin ciyayi, da man kare jiki daga hasken rana su ma sun karu matuka, ban da haka, wasu kayayyakin da ake amfani da su yayin yawon shakatawa su ma sun karu, jami'in dake kula da alkaluman kamfanin Suning Sun Liang ya bayyana cewa,

"Yayin bikin hutun ranar ma'aikatan kasa da kasa na bana, jama'a sun fi son zuwa wuraren bude ido da motocinsu, mun lura cewa, kayayyakin da ake bukata yayin yawon shakatawa da kamfanin Suning ya sayar sun karu sosai idan aka kwatanta da watan da ya gabata, misali kayan goge hakora yakaru da kaso 94.12 bisa dari, tawul din gode jiki ya karu da kaso 39.29 bisa dari, ruwan kasha kwayar cuta ya karu da kaso 51.73 bisa dari."

Shehun malama dake aiki a cibiyar sa kaimi kan sayayya ta ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Chen Lifen tana ganin cewa, yanzu haka ana dawowa bakin aiki daga duk fannoni a kasar, shi ya sa al'ummun kasar su ke sayen karin kayayyakin da suke bukata, ana iya cewa, yanayin sayayya mai inganci da kasar Sin ke ciki ba zai sauya ba, tana mai cewa,

"Ana ci gaba da dawowa bakin aiki daga duk fannoni a wurare daban daban na kasar Sin, haka kuma gwamnatin kasar tana aiwatar da manufofin gatanci domin ingiza sayayya a kasar, a sanadin haka, kasuwar sayayya a kasar tana kara habaka, sayayya ta intanet ita ma yana karuwa cikin sauri, a don haka, ana iya cewa kasuwar cikin gidan kasar tana kara karfi."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China