Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada bukatar tunkarar kalubale a yaki da ambaliyar ruwa don kare rayuka da dukiyoyin jamaa
2020-07-13 09:44:18        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a kara zage damtse don tunkarar duk wani kalubale da ka iya kunno kai, kana a dakile matsalar ambaliyar ruwa da gudanar da ayyukan ceto da rage radidi a kokarin ganin an kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban kwamitin kolin shugaban kasar, ya bayyana haka ne, cikin umarnin da ya bayar kan matakan da aka dauka, don shawo kan matsalar ambaliyar ruwa da aikin ceto.

Ya ce, kasar Sin ta shiga wani lokaci mai sarkakiya na tunkarar matsalar ambaliyar ruwa, a don haka ya bukaci kwamitocin jam'iyya da gwamnatoci a matakai daban-daban, da su dauki matakan da suka dace wajen kasancewa a wuraren da ake fama da wannan matsala don ba da jagoranci kan aikin shawo kan ambaliyar.

Shugaba Xi ya ce, yayin da ake daukar matakan shawo kan matsalar ambaliyar ruwa da aikin ceto, a hannun guda kuma, ya kamata kananan hukumomi su tsara matakan sake gina wurare da dawo da ayyuka da taimakawa jama'a wajen ganin sun koma gudanar da harkokinsu ba tare da bata lokaci ba.

Bugu da kari, wajibi ne a dauki managartan matakai don taimakawa matalauta da ambaliyar ta shafa, don ganin ba su sake komawa matsalar kangin talauci sakamakon wannan bala'i ba. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China