2020-07-12 16:34:30 cri |
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike sakon taya murna ga takwaransa na jamhuriyar Kiribati, Taneti Maamau bisa cika shekaru 41 da samun 'yancin kan kasar a ranar 12 ga watan Yuli.
Cikin sakonsa, shugaba Xi ya ce a yayin muhimmin lokaci na murnar cika shekaru 41 da samun 'yancin kan jamhuriyar Kiribati, a madadin gwamnatin Sin da al'ummar Sinawa, shugaban ya mika sakon taya murna da fatan alheri ga gwamnati da al'ummar kasar Kiribati. A ranar 27 ga watan Satumbar shekarar 2019, Sin da jamhuriyar Kiribati sun maido da huldar diflomasiyyar dake tsakaninsu, matakin da ya bude sabon shafi game da huldar dake tsakanin bangarorin biyu. Tun bayan farfadowar diflomasiyyar kasashen, bangarorin biyu suke kara zurfafa amincewa da juna, sun kaddamar da yarjejeniyoyi masu yawa domin amfanawa juna, da karfafa mu'amala tsakanin mutum da mutum, da musayar al'adu a tsakanin kasashen biyu, lamarin da ya haifar da babbar moriya ga jama'ar kasashen biyu. Shugaba Xi ya ce, yana dora muhimmanci game da bunkasuwar alakar dake tsakanin kasashen biyu kuma yana son yin aiki tare da bangaren Kiribati domin karfafa tattaunawa, da yin musaya, gami da hadin gwiwa daga dukkan fannoni, da kuma ingiza dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon mataki.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China