Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: A shirye kasar Sin take ta hada kai da Rasha wajen goyon bayan juna
2020-07-08 20:51:38        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, a shirye kasarsa take ta ci gaba da yin aiki da bangaren Rasha wajen goyon bayan juna, da kin amincewa da zagon kasa da tsoma bakin kasashen waje kan harkokin cikin gidansu.

Shugaba Xi wanda ya bayyana haka Larabar nan yayin da yake zantawa da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ta waya, ya ce a shirye kasarsa take da yin aiki da Rasha don kare cikakkun yankunansu da tsaro da ikonsu na samun ci gaba, da ma muradunsu na bai daya.

A nasa bangare shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha, ya bayyana cewa, kasarsa tana goyon bayan matakan kasar Sin na tabbatar da tsaro a yankin musamman na Hong Kong.

Putin ya ce, bangaren Rasha yana adawa da duk wani mataki na keta ikon mulkin kasar Sin, yana kuma da imanin cewa, kasar Sin za ta iya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da makoma mai haske a yankin Hong Kong.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China