2020-07-08 15:19:06 cri |
Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da wasu daliban sashin Karamay dake jihar Xinjiang na jami'ar koyon ilmin man fetur ta kasar Sin suka aika masa. Daliban wadanda suka kammala karatunsu a jami'a, sun samu amsa daga shugaba Xi, inda ya amince da shawarar da suka yanke ta yin aiki a sassan daban-daban dake kan iyakokin kasar Sin, yana mai bayyana fatansa ga wadanda suka kammala karatu daga jami'o'i.
Shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, wadannan dalibai suna shan wahala saboda barkewar cutar COVID-19, sun kuma fahimci cewa, duk wani mutum dake son ya samu nasara, dole ne ya yi kokari. Ya ce ba wanda zai cimma burinsa ba tare da shan wahala ba. Don haka ake bukatar himma da gwazo, don cimma muradun farfado da al'ummar kasar Sin daga zuriya zuwa wata.
Shugaba Xi ya kuma yi fatan masu kammala karatu daga jami'o'in, za su yi iyakacin kokari, wajen sauke nauyin dake wuyansu, da kuma ba da gudunmawarsu ga sha'anin bunkasuwar kasar Sin, da JKS, har ma da jama'ar kasa baki daya. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China