Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta jinjinawa kwazon ma'aikatan jinya da sauran jami'an lafiya
2020-05-12 12:42:48        cri
Yayin da ake bikin ranar ma'aikatan jinya wato NAS a yau Talata, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta jinjinawa kwazon su tare da sauran jami'an lafiya.

Yayin wani taron manema labarai a Geneva da ya gudana a jiya, darakta janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce suna taya murnar ranar ma'aikatan jinya ta duniya, kuma ya kamata a jinjinawa kwazon dukkan jami'an lafiya a ko da yaushe, amma kuma, ranar ta su, rana ce mai matukar muhimmanci domin ranar ce ta yaba musu.

Ya ce kowa ya sani cewa, yayin da ake yaki da COVID-19, su ne a kan gaba, inda suke sanya rayuwarsu cikin hadari domin ceton mutane, kuma ba a lokacin da ake fama da COVID-19 kadai ba. Yana mai cewa, ma'aikatan jinya su ke zaman gada tsakanin tsarin kiwon lafiya da al'umma, kuma abun da suke yi ke nan tun bayan da aikin nasu ya samo asali.

A don haka ya ce, WHO na mika godewa da girmama dukkan ma'aikatan jinya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China