Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararren WHO: Nazarin da Sin take game da tushen cutar COVID-19 daga jikin dabbobi yana da muhimmanci ga duniya
2020-05-06 12:08:49        cri
Dr. Gauden Galea, wakilin hukumar lafiya ta duniya WHO a kasar Sin, a jiya Talata ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa hukumar WHO da kasar Sin sun yi hadin gwiwa wajen gano wasu ilimomi game da tushen cutar COVID-19 daga jikin dabbobi a watan Fabrairu, kana nazarin da kasar Sin ta yi zai taimaka wajen cike gibi domin kandagarkin barkewar makamanciyar wannan annoba a nan gaba.

Dr. Galea ya ce, kasar Sin tana da cibiyoyin gwaje-gwaje, da masana ilmin cutukan al'umma, da kuma fasahohin gudanar da wadanan ayyukan gwaje gwaje.

WHO ta sanar a ranar 1 ga watan Mayu cewa, kwamitinta na aikin gaggawa ya amince cewa annobar da ake fama da ita a halin yanzu ta kasance babbar barazanar lafiya ta gaggawa ga kasa da kasa, kana ta bada shawarar cewa hukumar ta WHO da kungiyar kula da lafiyar dabbobi ta kasa da kasa (OIE) da hukumar kula da abinci ta kasa da kasa (FAO) za su yi aiki tare domin gano tushen cutar daga jikin dabbobi. Wadannan shawarwari daga kwamitin gaggawa ya bi diddigin shawarwarin da ya baiwa WHO da kasar Sin a ranar 23 zuwa 30 ga watan Janairu domin gano tushen annobar daga jikin dabbobi.

"Dukkan hujjojin da ake da su a halin yanzu sun nuna cewa, cutar ta faru ne min indallahi sabanin wani dan adam ne ya kirkire ta," a cewar Dr. Galea, ya kara da cewa, masu bincike da dama sun yi kokarin gano yadda al'amomin cutar suke kuma hujjojin da suka samu sun nuna cewa cutar bata da alaka da kirkira daga dakunan gwaje-gwaje.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China