Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
China Focus: Asibitocin Wuhan sun warkar da dukkan masu cutar COVID-19
2020-04-27 10:51:28        cri
Bayan wahalhalun da aka fuskanta sama da watanni uku, birnin Wuhan, wajen da a baya annobar COVID-19 ta fi kamari, ya zuwa ranar Lahadi, asibitocin dake birnin sun kammala aikin jiyyar dukkan masu dauke da cutar COVID-19.

Mi Feng, kakakin ma'aikatar lafiyar kasar Sin ya fadawa taron manema labarai a Beijing cewa, an samu wannan gagarumar nasara ne sakamakon jajurcewa da aiki tukuru na jami'an lafiyar Wuhan da sauran jami'an lafiyar da aka tura daga sauran sassan kasar Sin.

Sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi ta nuna cewa, a halin yanzu an kusan dakile yaduwar annobar COVID-19 a cikin gidan kasar Sin.

An danganta nasarorin da aka samu bisa jerin tsauraran matakai da gwamnati ta dauka da ma hadin kan al'ummar kasar.

Daga ranar 23 ga watan Janairu, an killace birnin Wuhan wanda ya shafe tsawon kwanaki 76 a kulle.

Shugabannin kasar Sin sun sha nanata aniyarsu ta mayar da rayukan jama'a da kuma lafiyar al'ummar kasar bisa matsayin koli, kuma hukumomin sun bada umarnin kula da dukkan majinyata sannan sun ce kada a bar ko da mutum guda ba tare da an bashi cikakkiyar kulawa ba.

A birnin Wuhan, an kafa asibitocin wucin gadi masu yawa domin jinyar mutanen da suka kamu da annobar COVID-19 kimanin asibitocin wucin gadi 16 aka bude, wanda ke kunshe da gadaje kimanin 60,000 don kula da majinyatan.

Sama da jami'an lafiya 42,000 aka tura zuwa lardin Hubei daga sassa daban daban na kasar Sin, kuma an tura kayan ayyukan kiwon lafiya da suka hada da na'urar taimakawa numfashi, da rigunan bada kariya ga jami'an lafiya, da takunkumin rufe fuska, da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China