Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta tallafawa WHO da karin dalar Amurka miliyan 30
2020-04-23 20:03:18        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce mahukuntan kasar Sin, sun yanke shawarar tallafawa hukumar lafiya ta duniya WHO, da karin kudi har dalar Amurka miliyan 30, kudaden da ake fatan amfani da su, wajen agazawa tsarin kiwon lafiyar kasashen duniya da dama. Geng Shuang ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba yi, na yau Alhamis.

Ko da a watan Maris da ya gabata ma, sai da kasar Sin ta baiwa hukumar ta WHO tallafin kudi har dalar Amurka miliyan 20, wadanda aka yi amfani da su, wajen karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin yaki da wannan cuta ta COVID-19, da kuma taimakawa kasashe masu tasowa, inganta ikon su na tunkarar wannan annoba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China