Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta soki kalmar da Pompeo ya yi amfani da ita domin zargin kasar
2020-04-24 19:21:55        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce bai dace sakataren wajen Amurka Mike Pompeo, ya rika amfani da kalmomi na yaudara ba.

Geng, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema larabai na rana rana da aka saba gudanarwa na Juma'ar nan, na tsokaci ne game da tambayar da aka yi masa, mai nasaba da zargin da Mr. Pompeo ya furta a jiya Alhamis, cewa mai yiwuwa kasar Sin tana da masaniyar bullar cutar COVID-19 a cikin gida tun cikin watan Nuwambar bara.

Gama da hakan, Geng ya ce ya kamata Mr. Pompeo ya san cewa, jaddada kalmar "mai yiwuwa" cikin wadancan kalamai na sa, ba za su yaudari kowa ba. Jami'in ya ce Sin na jaddada matsayin ta, na musayar bayanai a bayyane, da ma sauran matakai da ta aiwatar na kandagarki, da shawo kan cutar COVID-19 a cikin gida, da ma yadda take taka rawa a fannin hadin gwiwar yakin da duniya ke yi da wannan cuta.

Daga nan sai Mr. Geng ya ce tuni kasar Sin ta fayyace dukkanin batutuwa masu kunshe da muhimman matakai, na kandagarki da kuma shawo kan cutar tun bullar ta zuwa yanzu, wanda hakan ke nuna cewa, kalaman Mr. Pompeo ba su da tushe ko makama. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China