Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mai'aikatar wajen Sin: Babu kasuwannin namun daji a kasar Sin
2020-04-23 20:25:58        cri
A yau Alhamis ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labarai a nan birnin Beijing cewa, babu wata kasuwa ta sayar da namun daji masu rai a kasar Sin.

Kalaman na sa na zuwa ne, bayan da a jiya sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya yi kira ga kasar Sin, da sauran kasashe, da su rufe kasuwannin sayar da namun daji masu rai, domin rage kalubalen da bil Adama ke fuskantar.

Game da hakan, Geng Shuang ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta riga ta kafa doka, inda a cikin ta aka tanadi hana farauta, da ciniki, da jigila, da kuma cin namun daji, Ya ce kasuwannin sayar da nama, da kayan lambu, da 'ya'yan itatuwa na kasar Sin, ba kasuwannin sayar da namun daji ba ne, kuma duk wanda aka kama yana sayar da namun daji a kasuwanni, za a hukunta shi bisa doka. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China