![]() |
|
2020-04-25 16:40:22 cri |
Da yake zantawa da wakilin kafar yada labarai ta CMG, darektan hukumar lafiya ta kasar Sin Ma Xiaowei, ya ce kasar Sin ta kara samun gogewa wajen kula da marasa lafiya masu tsanani sanadiyyar barkewar cutar COVID-19, kuma za ta iya gabatar da fasahohinta ga duniya.
Ya ce adadin wadanda suka kasance cikin yanayi mai tsanani a asibitin Wuhan da ya kai matsayin koli a ranar 19 ga watan Febreru da mutane 9,689, ya dawo yanzu babu ko daya, kuma jimilar mutanen da suka warke a Wuhan ya kai kaso 92.2 cikin dari.
Ya ce kasar Sin ta kara samun gogewa bisa yanayi mai tsanani da ta shiga sanadiyyar COVID-19, wanda ya samar da ingantaccen tsarin da zai maye gurbin fannin kula da yanayi mai tsanani, ciki har da wadanda suka shafi numfashi da cututtuka masu tsanani da masu yaduwa, sannan yanayin ya tattaro jami'an lafiya sama da 42,000 dake taimakawa a wurare daban-daban cikin tsanaki, da hada ayyukan likitoci da na masu jinya da ayyukan samar da magani da kuma tabbatar da daidaito wajen kula da marasa lafiya
Darektan ya ce, baya ga karfin tunkarar cuta irin wannan da ka iya barkewa a nan gaba da wadannan fasahohi suka samar, za kuma a iya yayata su ga sauran sassan duniya. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China