![]() |
|
2020-04-22 20:45:03 cri |
Geng Shuang wanda ya yi wannan tsokaci a yau Laraba, ya ce kungiyoyi masu zaman kan su dake Sin, sun riga sun fara ba da tallafi ga kasashen waje, matakin dake nuni ga al'adar gargajiya ta al'ummar Sinawa.
A kwanakin baya an tambayi hamshakin dan kasuwar nan na kasar Sin Jack Ma, game da ra'ayin sa don gane da masu sukar tallafin da Sin ke samarwa ga kasashen duniya, inda ya ba da amsa da cewa, wawayen dake irin wannan suka ba su wuce kaso 1% na jimillar al'ummun kasashen da suke samun tallafin ba, don haka bai dace a mayar da hankali kan su, a bar kaso 99% na masu hankali ba. Kalaman da kuma a wannan lokaci shi ma Mr. Geng Shuang ya sake nanatawa. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China