Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilan ofisoshin jakadancin kasashen Afrika a Guangzhou sun amince da matakan yaki da COVID-19 na lardin Guangdong
2020-04-19 21:40:28        cri

Da yammacin ranar 18 ga watan Afrilu, wakilan kananan ofisoshin jakadancin kasashen Afrika da dama dake birnin Guangzhou na lardin Guangdong na kasar Sin sun yi hira da manema labarai. Sun nuna cikakkiyar gamsuwa bisa ga kokarin da lardin Guangdong ke yi game da matakan kandagarki da yaki da annobar COVID-19, sun bayyana cewa, annobar ba ta la'akari da banbancin iyakokin kasashe, annobar COVID-19 ta kasance babban kalubalen dake addabar dukkan bil adama. A halin yanzu, kananan ofisoshin jakadancin kasashen Afrika da gwamantin lardin Guangdong suna ci gaba da tuntubar juna, kuma sun yi amanna cewa, yin aiki tare zai tabbatar da yin nasarar yaki da annobar COVID-19.

A halin yanzu, kananan ofisoshin jakadancin kasashen Afrika dake Guangzhou sun bullo da wasu shirye shiryen tuntubar juna tsakaninsu da gwamnatin lardin Guangdong da ta birnin Guangzhou, domin a samu hakikanin fahimta game da matakan yaki da annobar COVID-19 ta Guangdong da kuma tsare tsaren da suka shafi hadin gwiwa domin yaki da annobar, a cewar Alima Danfakha Gakou, shugabar wakilan kasashen Afrika dake Guangzhou, kana jami'ar dake kula da karamin ofishin jakadancin kasar Mali a birnin Guangzhou, ta bayyana cewa, aminantaka da hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afrika dawwamamme ne. Ta kuma nuna fatan dukkan bangarorin za su yi aiki tare domin dakile barazanar annobar, da kuma kiyaye lafiyar al'umma.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China