Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin: Kwayar cuta ce abokiyar gabar Amurka ba kasar Sin ba
2020-04-20 20:36:01        cri
Yau a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi cewa, kamar yadda sauran kasashen duniya suke, kasar Sin ita ma tana shan wahala sakamakon kalubalen da annobar COVID-19 ta haifar, kuma dole ne wasu Amurkawa su kara fahimtar cewa, wannan kwayar cuta ita ce abokiyar gabar Amurka ba kasar Sin ba.

Jiya 19 ga wata, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, kasarsa tana son tura ma'aikatanta kasar Sin, domin gudanar da bincike kan yanayin dakile yaduwar cutar a kasar, kana ya bayyana cewa, ya kamata kasar Sin ta sauke nauyin dake wuyanta kan yaduwar annobar.

Geng Shuang ya jaddada cewa, yayin da kasashen duniya suke fuskantar kalubalen kiwon lafiyar jama'a mai tsanani, ya dace su kara karfafa hada kai tsakaninsu, a maimakon sukar junan su. Ya kara da cewa, murar H1N1 ta barke a Amurka a shekarar 2009, ta kuma yadu zuwa kasashe 214, har ta hallaka mutane kusan dubu 200, amma shin ko an taba neman Amurka ta biya diyyar wannan hasara? Kana a shekarun 1980, an gano kwayar Aids a Amurka a karon farko, daga baya ta bazu zuwa fadin duniya, ko an nemi Amurka ta sauke wani nauyi kan hakan?

Jami'in ya ce, ana sa ran cewa, wadannan Amurkawa za su nuna biyayya ga hakikanin abubuwan da suka shafi kimiyya da ra'ayoyin jama'a, haka kuma su daina zargin kasar Sin, su yi kokarin ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, a bangaren kandagarkin annobar COVID-19. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China