![]() |
|
2020-04-20 20:48:50 cri |
Geng shuang wanda ya yi tsokaci kan wannan batu a Litinin din nan, ya sake jaddada cewa, batun cutar COVID-19, batu ne na kimiyya, wanda sam bai dace a siyasantar da shi ba. Ya ce ba wata shaida dake tabbatar da wancan zargi na jami'an Amurka. Don haka kasar Sin ke fatan irin wadancan mutane za su rika mutunta gaskiya, da kimiyya da ra'ayin al'ummun kasa da kasa.
Geng ya kara da cewa, cibiyar gwaje gwajen kimiyya ta Wuhan na da managarcin tsarin gudanarwa, kuma ba wani jami'in ta ko da guda daya da ya kamu da cutar COVID-19. Kaza lika jami'an cibiyar na aiki tukuru wajen aiwatar da bincike na kimiyya.
Ya ce furta zargi maras tushe da labaran kanzon kurege da wasu jami'an Amurka ke yi, ba zai haifar da komai ba sai illata binciken kimiyya, da gurgunta hadin gwiwar dake tsakanin masana kimiyyar Sin da na Amurka. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China