![]() |
|
2020-04-21 21:02:58 cri |
A yau Talata a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, sanarwar ta nuna wa al'ummun kasa da kasa matsaya guda da kasashe masu tasowa suka cimma, kuma ko shakka babu lamarin zai ingiza hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a bangaren dakile annobar.
Game da sukar da Amurka ta yi wa hukumar WHO kwanan baya kuwa, Geng Shuang ya yi nuni da cewa, "Bisa matsayinta na kasa wadda ta fi samar da kudi ga hukumar, Amurka tana ganin cewa, ya kamata hukumar ta bi umurninta, to sai dai kuma wannan ra'ayin nuna fin karfi ne, kuma a nata bangare, WHO tana nacewa ka'idar adalci, ba ta bin umurnin Amurka kadai, a don haka Amurkar ta daina samar da tallafin ta na kudi, wanda hakan ya zama wani kalubale. Bugu da kari, sukar da Amurka ke yi wa hukumar WHO ba shi da wani tushe, kuma matsin lamba ga hukumar WHO, shi ma ba zai samu amincewa daga al'ummun kasashen duniya ba."(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China