Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Majalisar jam'iyyun siyasar Afrika ya jinjinawa kokarin Kasar Sin na yaki da cutar COVID-19
2020-02-24 09:21:23        cri
Mukaddashin Sakatare Janar na majalisar jam'iyyun siyasar Afrika, Mohamed Yousif Abdallah, ya bayyana goyon baya ga kasar Sin a yakin da take da annobar cutar numfashi ta COVID 19.

Mohamed Yousif Abdallah, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua jiya Lahadi a hedkwatar majalisar dake birnin Khartoum na Sudan cewa, namijin kokarin da gwamnatin kasar Sin ta yi, ciki har da matakan kula da marasa lafiya da na kariya da na dakile yaduwar cutar, musammam hana shiga da fita daga birnin Wuhan domin dakile cutar, sun yi tasiri sosai wajen yaki da ita.

Ya ce an samu kyawawan sakamako daga matakan da aka dauka, domin yawan wadanda ke kamuwa da mutuwa sanadin cutar ya fara raguwa sosai. Yana kuma mai jinjinawa irin hadin kan da al'ummar Sinawa suka nuna yayin da ake tunkarar wannan cuta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China