Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Afirka ta Kudu ya yi tsokaci kan sakamako takwas da ba zai yiyu ba Amurka ta cimma
2020-02-20 20:42:12        cri
Kwanan baya sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya zargi tsarin siyasar kasar Sin, a don haka yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya a ranar 18 ga wata, jakadan kasar Sin dake Afirka ta Kudu Lin Songtian ya yi tsokaci kan sakamako guda takwas da ba zai yiwu ba gwamnatin kasar Amurka ta cimma, haka kuma ya yi bayani kan fifikon tsarin kasar Sin wanda ya taimaka matuka kan aikin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

Jakada Lin ya ce, sakamako guda takwas suna kunshi: na farko, al'ummun kasar Sin sun hana yaduwar cutar cikin gajeren lokaci karkashin jagorancin babban sakataren JKS Xi jinping, da ma hana yaduwarta zuwa sauran kasashen duniya, na biyu, an kammala aikin gina asibitocin jinyar wadanda suka kamu da cutar yaduwa guda biyu wadanda za su samar da gadajen jinya 2600 a birnin Wuhan a cikin kwanaki goma kawai, a sa'i daya kuma an gina asibitocin wucin gadi da yawansu ya kai 15 a fadin lardin Hubei, na uku, al'ummun kasar Sin da yawansu ya kai biliyan 1 da miliyan 400 sun zauna a gidajensu domin killace yaduwar cutar karkashin jagorancin JKS da gwamnatocin wurare daban daban a fadin kasar, na hudu, likitoci sama da dubu 32 sun tafi birnin Wuhan da sauran sassan lardin Hubei tare da kayayyakin da suke bukata cikin gaggawa bisa radin kansu don ba da gudummawa, na biyar, birane da larduna da yawansu ya kai 19 suna samar da tallafi kai tsaye ga birane 16 na lardin Hubei, don ganin bayan annobar cikin hanzari, na shida, gwamnatin kasar Sin ta fara gudanar da tsarin daidaita matsalar nan take a fadin kasar inda ta ware kudi har dalar Amurka biliyan 10 domin samar da isassun kayayyaki ga masu bukata yayin da suke kokarin dakile annobar, na bakwai, JKS ta kubutar da al'ummun kasar da yawansu ya zarta miliyan 800 daga kangin talauci a cikin shekaru 40 da suka gabata, yanzu haka za ta cimma burin kawar da talauci daga duk fannoni nan da karshen shekarar 2020, lamarin da ya taka rawar gani kan aikin rage talauci a duniya, inda ya kai kaso 70 bisa dari, na takwas, har kullum kasar Sin dake karkashin jagorancin JKS tana nacewa kan manufar samun ci gaba ta hanyar wanzar da zaman lafiya, ba ta taba kai hari ga wata kasa ba, ba ta taba mamaye yankin wasu kasashe ko kadan ba, haka kuma ba ta taba sa wani 'dan kasar waje ya rasa muhalli ba, tana yin zaman jituwa tare da sauran kasashen duniya baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China