Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar jami'an lafiya ta Sin a Sudan ta yi taron wayar da kai game da kandagarki da jinyar masu fama da COVID-19
2020-02-20 11:24:31        cri

Tawaga ta 35 ta jami'an lafiyar kasar Sin dake aiki a Sudan, ta gabatar da taron wayar da kai game da kandagarki, da aikin jinyar wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19.

Tawagar ta gudanar da wannan taron lakca ne a jiya Laraba, a wani asibiti dake birnin Khartoum, fadar mulkin kasar ta Sudan. Manufar taron dai ita ce inganta kwarewar jami'an lafiya a fannin gano alamun cutar cikin sauri, da bincike kanta, da samar da magani, wanda hakan zai amfani daukacin al'ummar Sudan. Taron dai ya samu halartar jami'an lafiya da kwararru daga kasashen Sin da na Sudan su sama da 50.

Da yake tsokaci game da irin nasarorin da kasar Sin ta samu, a fannin kandagarki da shawo kan yaduwar cutar COVID-19, daya daga cikin tawagar likitocin kasar Sin da ya halarci taron Dr. Li Changhong, ya ce tuni tawagarsa ta tattauna da ma'aikatar lafiyar Sudan game da wannan cuta, ta kuma ziyarci asibitin kwararru dake birnin Khartoum, domin duba matakan kandagarki, da shawo kan cutar, da ma na killace wadanda suka kamu da cutar da aka tanada.

A nasa bangare kuwa, wani kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa a ma'aikatar lafiyar kasar Sudan Dr. Nagah Mohamed, jinjinawa matakan da mahukuntan kasar Sin suka dauka ya yi, tun barkewar wannan annoba kawo yanzu. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China