Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya ya yi tsokaci kan hulda tsakanin Sin da sauran kasashen duniya bayan barkewar COVID-19
2020-02-19 19:16:45        cri

Jiya Talata ne, darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin dake tarayyar Najeriya Charles Onunaiju ya rubuta wani sharhi mai taken "Hulda tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya bayan barkewar cutar numfashi ta COVID-19" a jaridar Peoples Daily, inda ya yi tsokaci cewa, shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar ta kawo wa daukacin kasashen duniya, musamman ma kasashen Afirka manyan sauye-sauye, kana ya jaddada cewa, cutar numfashi ta COVID-19 annoba ce da ta shafi daukacin bil Adama, ko shakka babu kasar Sin za ta yi nasarar ganin bayanta karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, saboda tsarin kasar ta Sin yana da inganci matuka.

A cikin sharhin, malam Onunaiju ya bayyana cewa, barkewar cutar ba ma kawai ta kawo barazana ga kasar Sin ba, har ma ta kawo illa ga ci gaban kasashen duniya baki daya, a don haka hukumar lafiyar duniya wato WHO ta bukaci kasa da kasa su yi hakuri su hada kai domin dakile annobar tare. Amma wasu kasashen yamma, musamman ma wasu 'yan siyasar kasar Amurka ba su son ganin kasar Sin ta kubuta daga mawuyacin yanayin da take ciki ba, domin samun moriyarsu daga wannan annoba. Hakika kasar Sin tana da karfin dakile annobar karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tare kuma da tabbatar da kwanciyar hankali a kasar.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China