Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya ya yi kira da a goyi bayan Sin wajen yaki da cutar COVID-19
2020-02-23 16:36:18        cri
Masanin Najeriya Oweli Lakemfa ya wallafa wani sharhi a jaridar Vanguard kwanan baya mai taken "Hadin kan kasar Sin don yaki da cutar COVID-19", inda ya yi kira ga al'ummar kasarsa da kada su bar kasar Sin kadai wajen yaki da cutar, kamata ya yi a yi hadin kai a maimakon shafa mata bakin fenti, hakan zai dace da muradun jama'ar kasa da kasa.

Sharhi ya kuma nuna cewa, kasar Sin tana da alaka matuka da bunkasuwar kasa da kasa, suna da makoma iri daya. Sin tana bada gudunmawarta da ba za a iya mantawa ba a fannin ingiza bunkasuwar tattalin arziki da kawar da kangin talauci, wadda ta zama wani ginshikin ingiza bunkasuwar duniya baki daya. Idan Sin ta samu koma baya, zai illata duk duniya, saboda haka, kowane bangare yana da ruwa da tsaki kan yaki da cutar COVID 19. Kamata ya yi, kasashen duniya su nuna godiya bisa ga namijin kokarin da Sin take yi wajen yaki da kuma kandagarki cutar. Ban da wannan kuma, ya yi tambaya cewa, ko akwai sauran kasashe dake iya gina asibitoci 2 wadanda suke da gadaje 2600 cikin kwanaki 12? Kamar yadda kafar yada labarai ta Xinhua ta fada cewa, Sin tana yin abubuwan ban al'ajabi.

Ban da wannan kuma, bayani ya nuna cewa, babu ruwan bambancin ra'ayi ko ra'ayin siyasa a game da wannan cuta, haka kuma babu amfanin yada jita-jita da shafawa saura bakin fenti, hanya daya tilo da za a bi wajen magance wannan kalubale shi ne kasashen duniya su hada kansu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China