Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan za a nuna adawa ga kwayar cutar siyasa
2020-02-20 19:17:12        cri
Yau Alhamis 20 ga wata, mai magana da yawun ma'aikatar wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi ta yanar gizo cewa, kasarsa tana fatan kasashen duniya za su ci gaba da nuna adawa ga kwayar cutar siyasa kamar yada jita-jita marasa tushe yayin da suke kokarin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, wasu mutane da kafofin watsa labarai na kasashen yamma suna zaton cewa, watakila kasar Sin ce ta samar da kwayar cutar numfashin bisa shirinta na "makamai masu guba", har suna zargin cewa, kwayar cutar, ta fito daga dakinta na gwaje-gwajen makamai masu guba.

Geng Shuang ya bayyana cewa, a halin yanzu, al'ummun kasar Sin suna kokari matuka domin ganin bayan annobar numfashin, lamarin ba ma kawai zai kare lafiya ba, har ma zai kiyaye tsaron lafiyar jama'a a fadin duniya, amma a daidai wannan muhimmin lokaci, wasu mutane da kafofin watsa labarai sun baza jita-jita marasa tushe, da ma kokarin shafawa kasar Sin kashin kaza, bisa rashin sani ko ganganci saboda ba su san kome ba kan cutar.

Geng ya kara da cewa, sau tari jami'an hukumar lafiyar duniya sun bayyana cewa, babu shaida ko kadan da ta nuna cewa, kwayar cutar numfashi ta COVID-19 ta fito ne daga dakin gwaje-gwaje, ko kuma makami mai guba ne da kasar Sin ta samar, kana fitattun likitoci da dama na kasashe daban daban su ma suna ganin cewa, jita-jitar da aka baza kan batun ba su da tushe a bangaren kimiyya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China