![]() |
|
2020-02-20 13:05:02 cri |
'Yan uwa matan sunayensu Qi Meiyan, da Qi Meiling, dukkansu nas nas ne, a sashen kula da yara kanana na asibitin Shengjing mallakar jami'ar horar da likitoci ta kasar Sin. Tuni dai suka mika bukatar su ga asibitinsu, ta tafiya zuwa lardin Hubei don ba da tallafi, amma la'akari da hakikanin halinsu, asibitin ya yarda da wata daga cikinsu ta tafi Hubei, amma 'yan uwan matan sun tsaya kan ba da tallafi tare.
Qi meiyan yaya ce, wadda ta taba tsaida kudurin shirya bikin auren ta a ranar 1 ga watan Maris, amma ta jinkirta lokacin bikin sakamakon tafiya birnin Xiangyang, yayin da kanwata Qi Meiling ita ma ta jinkirta lokacin bikin auren ta da ake shirin yi a watan Aflilu, bayan tattaunawa da masoyinta. A ganinsu aikin yaki da cutar shi ne wani batu mafi muhimmanci. 'Yan uwan mata su biyu, suna kara wa juna karfin gwiwa, suna hada kai don yaki da cutar.
An ce, ya zuwa yanzu an riga an aika da likitoci da nas nas sama da dubu 30, daga sassan duk fadin kasar zuwa lardin Hubei. (Bilkisu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China