Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta dauki nauyin ta yadda ya kamata wajen yaki da cutar COVID-19
2020-02-20 16:24:13        cri

Ranar 20 ga wata, ita ce rana ta 29 tun bayan da aka rufe birnin Wuhan, wanda aka fi sani da cibiyar cutar numfashi ta COVID-19. Ban da babban yankin kasar Sin, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a sauran sassan duniya bai kai 1% ba, kuma cikin wadannan mutane, uku daga cikinsu sun rasu.

Bisa bayanin da hukumar kiwon lafiyar duniya wato WHO ta yi, an ce, sabo da matakan hana yaduwar cutar da kasar Sin ta dauka, cutar numfashi ta COVID-19 ba ta yadu zuwa wasu sassan duniya ba.

Amma, an taba nuna mabanbacin ra'yoyi kan matakin rufe birnin Wuhan mai kunshe da mutane miliyan 11. A hakika dai, an dauki wannan mataki ne domin hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 baki daya, kuma hanyar ceto a bude take a ko da yaushe. Kana ana ci gaba da tura ma'aikatan likitanci daga wurare daban daban na kasar Sin zuwa birnin Wuhan. Ya zuwa ranar 17 ga wata, gaba daya an tura ma'aikatan likitanci dubu 32, daga sauran wurare na babban yankin kasar Sin zuwa lardin Hubei.

Ya zuwa yanzu kuma, ana samun karin mutane dake nuna yabo ga kasar Sin, kan matakan hana yaduwar cutar da ta dauka, kuma akwai karin mutane da suka nuna amincewa kan babban kokarin da kasar Sin ta yi.

Jakadan kasar Canada dake kasar Sin Dominic Barton ya ce, ya amince da matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka, na rufe wannan birni mai kunshe da mutane miliyan 11 domin kare sauran mutanen kasar daga wannan cuta.

Wakilin WHO dake kasar Sin, Gauden Galea ya jaddada cewa, matakin kebe mutane a gidajen su da kasar Sin ta dauka, ya rage damar mu'amala a tsakanin mutane, wanda ya ba da taimako matuka wajen hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

Ko shakka babu, rufe birnin Wuhan ya dakatar da wasu harkoki, ya kuma haddasa babbar illa ga tattalin arzikin kasar.

A nasa bangaren, babban sakataren hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa, "matakin da kasar Sin ta dauka wajen hana yaduwar cutar daga asalinta ya burge mu kwarai da gaske, ko da yake Sin ta gamu da babbar asara, amma matakin ya baiwa wasu sauran kasashen lokaci, da kuma rage saurin yaduwar cutar a sauran kasashen duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China