Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sun Chunlan: Dole a yi iyakacin kokari wajen ceton wadanda suka kuma da cutar COVID-19
2020-02-20 13:06:37        cri

Kwanan baya, tawagar ba da jagoranci ta kwamitin tsakiya dake karkashin jagorancin Sun Chunlan, wakiliyar ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, kana mataimakiyar firaministan gwamnatin kasar Sin, ta kai ziyara a wasu asibitoci, inda suka yi mu'amala da likitoci, domin karfafa ayyukan ba da jinya ga masu fama da cutar numfashi ta COVID-19 mai tsanani, da masu fama da cutar maras tsanani. Haka kuma, sun ce, ya kamata mu yi iyakacin kokari wajen gudanar da aikin ceto, da kara shigar da masu dauke da cutar asibitoci, da kuma kara adadin mutanen da za su warke daga cutar. A sa'i daya kuma, a rage adadin masu kamuwa da ita, da wadanda za su mutu sakamakon kamuwa da cutar.

A halin yanzu, gaba daya akwai ma'aikatan likitanci sama da dubu 30 da aka tura zuwa birnin Wuhan na lardin Hubei daga wurare daban daban, da rundunar soja ta kasar, ciki har da likitoci na fannonin cutar numfashi, da cututtuka masu yaduwa, da ciwon zuciya da dai sauransu. Kana, a halin yanzu, ana da ma'aikatan likitanci na fannin cututtuka masu tsanani kimanin dubu 11 a birnin Wuhan, adadin da ya kai kaso 10% bisa dukkanin ma'aikatan likitanci na wannan fanni da ake da su a duk kasar ta Sin. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China