Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya gana da firaministan gwamnatin wucin gadi na Sudan
2019-09-25 14:50:23        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da firaministan gwamnatin wucin gadi na kasar Sudan Abdalla Hamdok, a yayin da yake halartar babban taron MDD da ake yi a birnin New York na kasar Amurka.

A yayin ganawar tasu, Wang Yi ya ce, a halin yanzu, kasar Sudan tana kan wani sabon matsayi na neman ci gaba, kuma kasar Sin tana goyon bayan kasar wajen neman 'yancin kanta da kuma kare cikakken yankinta, za ta kuma cigaba da ba da taimako ga kasar yadda ya kamata da kuma karfafa hadin gwiwar bangarorin biyu bisa fannoni daban daban.

Abdalla Hamdok ya ce, jama'ar kasar Sudan suna godiya matuka dangane da taimakon da kasar Sin ta samar mata wajen neman 'yancin kan kasashen Afirka, kiyaye tsaron nahiyar, da kuma neman ci gabanta. Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, gwamnatin kasar Sudan tana dukufa wajen kiyaye zaman karkon kasa da neman ci gaba, tana fatan samun taimakon kasar Sin a wannan fanni. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China