Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Makalawa Sin sunan mai magudi game da darajar kudin ta zubar da kimar Amurka ne in ji wani tsohon jami'in kasar
2019-08-07 14:15:17        cri
Tsohon sakataren baitulmalin Amurka, kuma mashawarci ga shugaba Barack Obama a gwamnatin Amurka da ta shude Lawrence Summers, ya zargi sakataren baitulmalin Amurka mai ci Mr. Steven Mnuchin, da makalawa Sin sunan mai magudi ta fuskar darajar kudin ta, matakin da ya ce ya zubar da kimar Amurka a idon duniya.

Cikin wani sako na bayyana ra'ayi da aka wallafa a jaridar Washington Post, Mr. Summers, wanda shaihun malami ne dake koyarwa a jami'ar Harvard a Amurka, ya ce kalaman sakataren baitulmalin Amurkan na baya bayan nan game da kasar Sin, sun nuna yadda ya zubar da darajar ofishin sa, ko da yake dama hakan ya yi daidai da manufofin shugaban kasar mai ci.

Ya ce " A yanzu abu ne mai wuya, yanayin kasuwannin hada hadar kudi ya gaskata zargin da sashen baitulmalin Amurka ya yi, kuma a zahiri take cewa, dan raguwar daraja da kudin Sin yuan ya samu a ranar Litinin, ba wani kagaggen lamari ba ne, ana ma iya cewa sakamako ne na karin haraji da Amurka ta kakabawa hajojin Sin da ake shigarwa Amurkar". (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China