Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya gana da takwaransa na Amurka
2019-08-01 20:03:42        cri
Memban majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Amurka Mike Pompeo yau Alhamis a birnin Bangkok na kasar Thailand.

Yayin zantawar tasu, Wang ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping da shugaba Donald Trump na Amurka, sun cimma matsaya daya a fannoni da dama, a yayin shawarwarin da suka yi a watan Yunin bana a birnin Osakar kasar Japan, wanda hakan ya kafa alkibla ga ci gaban dangantakar kasashen biyu. Ya ce ya kamata Amurka ta hada kai tare da kasar Sin, don tabbatar da matsaya da shugabanninsu suka cimma.

A nasa bangaren, Mike Pompeo ya ce, Donald Trump gami da gwamnatinsa, ba su da niyyar kawo tsaiko ga bunkasuwar kasar Sin, har ma suna fatan fadada hadin-gwiwa da Sin a bangarori daban-daban, da ci gaba da ciyar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu gaba. Pompeo ya jaddada cewa, kasarsa za ta ci gaba da mutunta wasu sanarwa uku da aka daddale tsakanin Sin da Amurka, gami da manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duk fadin duniya. Ya ce Amurka na goyon-bayan inganta mu'amalar al'adu tsakanin kasashen biyu, kuma tana fatan shawo kan matsalolin da suka kunno kai a yayin mu'amalarsu. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China