Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jirgin ruwan yakin Amurka ya lalata jirgin Iran maras matuki a mashigin Hormuz
2019-07-19 10:23:47        cri
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar a jiya Alhamis cewa, jirgin ruwan yakin kasarsa ya yi nasarar lalata jirgin Iran maras matuki a zirin Hormuz.

Da yake jawabi a fadar White House, Trump ya ce, jirgin ruwan yakin Amurkar samfurin USS Boxer, ya lalata jirgin yakin Iran maras matuki, bayan da ya yiwa jirgin ruwan yakin Amurkar barazana ta hanyar yin shawagi a nisan da bai gaza yadi 1,000 ba a samansa.

Trump ya ce, jirgin Iran maras matukin yana barazana ga lafiyar jirgin ruwan yakin na Amurka da matukansa, inda ya kira kakkabo jirgin a matsayin matakin kare kai.

Daga bisani, babban mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, Jonathan Hoffman ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, jirgin ruwan yakin Amurka, ya kakkabo jirgin Iran maras matuki ne da misalin karfe 10 na safe agogon wurin, lokacin da yake kokarin yada zango a mashigin Hormuz.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China