Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An saukar da tutoci zuwa rabin sanda a Amurka don makokin wadanda suka rasa rayuka a wasu hare-haren bindiga
2019-08-05 13:10:51        cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump a jiya Lahadi ya bukaci hukumomin kasar da su saukar da tutoci zuwa rabin sanda, har zuwa ranar 8 ga watan da muke ciki, don nuna alhinin rasuwar mutane sakamakon hare-haren bindiga da suka abku a kasar a karshen mako.

Shugaban ya ce, daukacin al'ummun kasar za su yi zaman makoki tare da iyalan wadanda suka rasa rayuka a hare-haren da aka yi a biranen El Paso da Dayton, sa'an nan suna Allah wadai da hare-haren da aka yi, inda aka nuna wani yanayi na kiyaya, da kuma rashin karfin zuci.

Sai dai, ko da yake shugaban ya yi tir da munanan hare-haren cikin jawabinsa, amma jama'ar kasar ba su gamsu ba, ganin yadda gwamnatin kasar ta nade hannu ba tare da daukar wani mataki na tsaurara matakan kula da bindigogi ba. An ce, yadda aka ba jama'a damar samun bindiga cikin 'yanci, shi ne dalilin da ya sa a kan samu hare-haren bindigogi a kasar. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China